Hukumomi a Najeriya sun ce mutane 18 sun mutu a Kaduna

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption sojojin najeriya a wajan tashin bam

Hukumomi sun tabbatar da harin bam da ya afku a Kadunan Najeriya kuma sun ce akalla mutane goma sha takwas sun rasa rayukansu a harin kunar bakin wake da akai amfani da motoci biyu

Wani jami'i ya shaidawa BBC cewa abin hawa ya tarwatse ne a wurin da yake da jamaa da dama a birnin.

Ya ce bam din na da karfin gaske yadda injin motar da ta tarwatse da dan kunar bakin waken, ya kai mita hamsin tsakanin wajan da akayi harin da inda aka sameshi.

Andai tsaurara matakan tsaro a Kaduna a yan kwanakin nan tun gargadin da Boko Haram su kayi cewa za su kai hari a birnin.

Boko Haram dai ta sha daukar nauyin hare hare mai kama da wannan, amma har izuwa yanzu ba wanda ya dauki nauyin kai wannan harin.

Kuma an kai harin ne a dai dai lokacin da ake bikin Easter a fadin kasar.

Ko a lokacin bikin Kirsimati an kai mummunan harin bakin wake a Cocin Catholic dake Madalla, kusa da birnin Tarayya Abuja, abunda yayi asarar rayuka da dama wasu kuma suka jikkata.

Karin bayani