'Yan sanda a Najeriya sun ce mutane biyar ne suka rasu a Kaduna

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption mota na konewa a harin bam

Jami'an yan sanda sun ce mutane biyar suka rasu, goma sha shida suka ji rauni a harin kunar bakin wake da aka kai a Jihar Kadunan Najeriya.

Sai dai wata majiya daga Hukumar bada agaji ta ce akalla mutane goma sha takwas sun rasu a harin inda galibi masu sana'ar achaba da masu sayar da abinci ne harin ya fi rutsawa da su.

Jami'an tsaro sun ce mai kokarin kai harin a mota ya gaza samun damar kutsawa wata coci ne inda ya koma ya tada bam din a sha tale talen kusa da filin wasa na Kaduna.

Jamia'n tsaro dai sun killace wuraren da alamarin ya faru gami da kara matakan tsaro a wasu sassa na Jihar don gudun sake afkuwar harin.

Boko haram dai ta sha daukar nauyin hare haren mai kama da wannan, amma har izuwa yanzu ba wanda ya dauki nauyin kai harin.

Kuma an kai harin ne a dai dai lokacin da ake bikin Easter a fadin kasar.

Ko a lokacin bikin Kirsimati an kai mummunan harin kunar bakin wake a Cocin Catholic ta garin Madalla dake kusa da birnin Tarayya Abuja, abunda yayi asarar rayuka wasu kuma suka jikkata.

Karin bayani