Mutane akalla 38 suka mutu a harin Kaduna

Harin bam a Kaduna
Image caption Harin bam a Kaduna

Masu ayyukan agaji na gaggawa a Najeriya sun ce, akalla mutane talatin da takwas ne aka kashe sakamakon harin bama-bamai da aka dana a mota a garin Kaduna dake arewacin kasar.

Kakakin hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kadunan, Abubakar Zakari Adamu ya fadawa BBC cewa, wasu da dama sun jikkata sakamakon harin, kuma lamarin yayi mummunan ta'adi a wannan bangare na garin Kaduna.

Wakilin BBC ya ce, bama-baman biyu sun yi ta'adi inda suka hallaka 'yan achaba da mabarata, da kuma wasu da suka fito motsa jiki da sassafe.

Tun a kwanakin baya dai kungiyar Boko Haram ta fitar da wata takarda inda take gargadin hukumomi a jihar ta Kaduna da su sako ma ta mutanenta da ta ce ana tsare da su, tana mai barazanar kai hare hare idan aka ki yin hakan.

Ko a kwanakin baya wani abm ya tashi da wani da ake zargin dan kungiyar ne, yayinda yake kokarin dana shi a jikin wata tankar daukar mai a Kadunan.

Karin bayani