Babban jami'in 'yan sandan Koriya ta Kudu ya yi murabus

Shugaban Korea ta Kudu Lee Myung Bak Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Babban jami'in 'yan sandan Koriya ta kudu ya ajiye aikinsa

Babban jami'in hukumar 'yan sandan Kasar Koriya ta Kudu ya sauka daga kan mukaminsa, biyo bayan koken da jama'a suke ta yi game da fyaden da akai wa wata mata, daga bisani kuma aka hallaka ta, duk kuwa da cewa ta kira wayar 'yan sanda a lokacin da take cikin tashin hankalin

Cho Hyun-Oh yace ya dauki alhakin abinda ya kira sakacin aiki na ma'aikatansa

Matar dai ta bada cikakken bayanin inda take zaune, amma sai da 'yan sandan suka shafe sa'oi kafin su gano inda take, a lokacin da suka isa kuma, rai yayi halinsa.

An dai tsare wani mutum guda da ake zargi