'Yan bindiga sun kai hare-hare a Najeriya

Maiduguri Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Birnin Maiduguri ya sha fama da hare-haren kungiyar Boko haram

A Najeriya wasu 'yan bindiga sun kai hari a garin Dikwa da ke jihar Borno a Arewa maso gabshin kasar, inda suka kashe mutane uku ciki harda tsohon shugaban karamar hukumar ta Dikwa Babagana Ali Karim da kuma wani jami'in 'yan sanda.

Rundunar samar da zaman lafiya ta hadin gwiwa wato JTF a jihar ta Borno ta tabbatar da afkuwar wannan lamari, inda ta ce ta kashe uku daga cikin maharan - wadanda ta zarga da kasancewa 'ya'yan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram.

Mai magana da yawun rundunar samar da zaman lafiyar ta JTF, Lafatanal Kanal Sagir Musa, ya ce maharan sun kona ofishin 'yan sanda na Dikwa da bankin Unity da Otel din Freedom da kuma ginin sakatariyar karamar Hukumar ta Dikwa, a wani hari da suka kaddamar a yankin da sanyin safiyar ranar Litinin.

A garin Potiskum na jihar Yobe mai makwaftaka da Maidugurin kuma, rahotanni sun ce wasu 'yan bingida sun bude wuta kan iyalin wani jami'in 'yan sanda inda suka kashe 'yarsa mai shekaru shida da haihuwa.

'Mun kwace makamai'

A jihar Kano da ke arewa maso yamma kuwa, jami'an tsaro a jihar ne suka ce sun yi nasarar gano wani bam da aka dana a gefen hanya, inda daga bisani suka tayar dashi ba tare da samun asarar rai ko jikkata ba, bayan da aka kwashe jama'a daga yankin.

Kanal Musa ya ce rundunarsu ta yi nasarar da dakile kaifin harin na Dikwa, bayan da ta kashe uku daga cikin maharan yayin da wasunsu da dama suka tsere da raunukan bindiga a jikinsu.

"Mun kwace makamai da alburusai da dama da kuma wata mota daga hannun 'yan bindigar wadanda ya ce 'ya'yan kungiyar nan ne da aka fi sani da Boko Haram," a cewarsa.

Wadannan lamara na faruwa ne sa'o'i kadan bayan mummuanharin bam din da aka kai a garin Kaduna wanda ya yi sanadiyyar mutuwar kusan mutane 40 a jiya Lahadi.

Karin bayani