Mutane sun mutu a fashewar bam a Somalia

Hakkin mallakar hoto AFP

A kalla mutane goma sha daya sun hallaka a wani tashin bam a garin Baidoa dake tsakiyar Somalia.

Gwmanan lardin ya shaidawa BBC cewa fiye da mutane 30 ne lamarin ya rautana, kuma cikinsu harda maata da yara kanana.

Gwamnan ya ce kungiyar Al-shabba ce ta kai harin, yana mai bayyanata da cewa ta 'yan tadadda ce.

Bam din ya fashe ne a cikin wata kasuwa a lokacinda take ci dazu da rana.

A watan Fabrairu ne dakarun Habasha suka kwace iko da garin daga hannaun kungiyar Al-shabbab

Karin bayani