An hallaka mutane sama da dari a Syria

Hakkin mallakar hoto AP

A kalla mutane dari ne masu fafutuka a Syria suka ce an hallaka bayan da dakarun tsaro suka bude masu wuta ta sama da jirage masu saukar ungulu.

Harin dai shine mafi muni tun bayan da aka fara zanga-zangar nuna adawa da gwamnati a kasar.

Can dama dai ana zaman dar-dar a akan iyakar Turkiyya da Syria a yayinda ake cigaba da nuna rashin tabbas akan shirin zaman lafiyar kasar da zai fara aiki gobe Talata.

Tun farko Turkiyyya ta ce dakarun Syria su daina yin harbi kan iyakar ta.

Amurka ta nuna damuwa matuka, akan yadda Syria ta yi harbi akan sansanin masu gudun Hijira a cikin Turkiyya.

Maikaitar harkokin Wajen Turkiyya ta ce harbin na nufin wa'adin gobe talata da aka baiwa dakarun Syria na su fice daga wuraren da farar hula keda yawa, yanzu bazaiyi aiki ba.

Kakkakin ma'akatar harkokin wajen Turkiyya ya shaidawa BBC cewa sun bukaci bayani daga Syria akan harbin;

Karin bayani