Za a iya mika Abu Hamza ga Amurka

Abu Hamza Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Abu Hamza

Kotun kare hakkin bil'adama ta Tarayyar Turai za yanke hukuncin cewa Burtaniya za ta iya mika wasu mutane shida da ake zargi da ayyukan ta'addanci ga Amurka.

Burtaniya ce dai ta bukaci tasa keyar mutane shida da ake zargi da ayyukan ta'addanci ciki har da fitaccen malamin addinin Musulunci Abu Hamza zuwa Amurka.

A can ne ake sa ran yanke musu hukuncin daurin shekaru da dama na zaman kadaici.

Wadanda ake zargin sun je kotun ne domin hana hukumomin Burtaniya tasa kyayarsu zuwa Amurka.

Fira Ministan Burtaniya David Cameron ya ce ya yi farin ciki da hukuncin kotun.

Shi dai Abu Hamza wanda dan asalin kasar Masar ne, a halin yanzu yana zaman kaso na shekaru bakwai a Burtaniya bayan da aka same shi da laifin cusa kyamar jinsi a tsakanin mutane.