An sace jami'in diplomasiyya na Costa Rica

Shugabar kasar Costa Rica, Laura Chinchilla Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugabar kasar Costa Rica, Laura Chinchilla

'Yan sanda a Venezuela suna kokarin nemo Guillermo Cholele, jami'in huldar diplomasiyya na Costa Rica da aka sace a daren ranar lahadi.

Jami'in wanda aka sace a gaban gidansa dake Caracas lokacin da ya shiga motarsa, an nemi a biya kudin fansa, muddin ana son a sako shi.

Mataimakin ministan harkokin wajen Costa Rica, Carlos Rovessi ya ce, babban abin damuwar sa ita ce lafiyar jami'in diplomasiyyar, saboda yana da matsaloli na ciwon zuciya da hawan jini.