Joyce Banda ta kori shugaban 'yansanda

shugaba Joyce Banda Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption shugaba Joyce Banda

Kwanaki bayan rantsar da ita, sabuwar shugabar Malawi, Joyce Banda ta jaddada ikon ta.

A yau ta sallami wasu manyan jami'an gwamnati biyu.

Abu na farko da ta yi bayan ta kama aiki kwanaki hudun da suka wuce shi ne sallamar shugaban rundunar 'yan sandan kasar, Peter Mukhito.

A wani taron manena labarai, Mrs Banda ta kuma yi bayani akan yadda take shirin tunkarar matsalolin tattalin arzikin kasar.

Ranar Asabar aka rantsar da Joyce Banda a matsayin mace ta farko da zamo shugabar kasar ta Malawi, bayan rasuwar shugaba Bingu Wa Mutharika.

Shugaba Mutharika ya rasu ne a sakamakon ciwon zuciya.

An kuma ta yin jayayya dangane da wanda zai gaje shi, ganin yadda aka mayar da Joyce Banda saniyar ware, a gwamnatinsa, duk da ake ita ce mataimakiyar shugaban kasa.

Karin bayani