An janye gargadin yiwuwar afkuwar Tsunami

Jama'a a titunan Banda Aceh Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hankalin jama'a ya tashi a sassa da dama na gabar kogin India

An dage gargadin da aka sanya na yiwuwar afkuwar bala'in tsunami a gabar kogin India bayan da aka samu girgizar kasa a yankin Aceh na kasar Indonesia.

Sa'o'i biyu bayan girgizar kasar - mai karfin maki 8 da digo 6 da kuma maki 8 da digo 3 - hukumar kula da gargadin tsunami ta yankin Pacific ta ce hadarin ya kau.

Gargadin da aka bayar ya jefa mutane cikin rudani inda jama'a suka rinka barin gidajensu.

India da Sri Lanka duka sun janye na su gargadin da suka bayar.

Sai dai kawo yanzu babu rahotannin asara ko kuma barna.

Yankin ya sha fama da bala'in Tsunami akai-akai. Bala'in Tsunamin da ya afku a shekara ta 2004 ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 170,000 a Aceh kadai, da kuma mutane 250,000 a yankin baki daya.

Hukumar kula da yanayi da Amurka (USGS), wacce ke sanya ido kan girgizar kasa a fadin duniya, ta ce girgizar kasar ta Aceh ta faru ne kimanin kilomita 495 daga Banda Aceh, babban birnin yankin.

Wakiliyar BBC a Karishma Vaswani a birnin Jakarta, ta ce an samu rahotannin gine-gine sun rinka juyawa har tsawon mintina biyar.

Akwai yiwuwar barna

Gargadin PTWC ya ce akwai yiwuwar tsunami kuma za ta iya yin barna matuka, sai dai ba a bayyana wuraren da abin zai shafa ba.

Shugaban kasar Indonesian Susilo Bambang Yudhoyono ya shaida wa manema labarai a Jakarta, cewa kawo yanzu babu rahotannin tsunami, "sai dai muna cikin shirin kota-kwana".

"Shirinmu na gargadi na aiki kamar yadda yakamata, na kuma umarci jami'an aikin agaji da su garzaya Aceh domin shawo kan lamarin", a cewarsa.

Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP a Banda Aceh ya ce an samu karamar girgizar kasa ta tsawon mintina hudu.

Hukumomi a Amurka da India sun sassauta gargadin da suka yi na afkuwar bala'in tsunami.

Karin bayani