Mali na gab da komawa mulkin farar hula

shugaban Mali mai jiran gado Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption shugaban Mali mai jiran gado

Kotun kolin kasar Mali ta share fage ga kakakin majalisar dokokin kasar na karbar ragamar shugabancin kasar na riko.

A ranar Alhamis ne za a rantsar da Dioncounda Traore, wanda zai mayar da kasar kan tafarkin mulkin farar hula, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan jiya.

Babu cikakken bayani game da irin rawar da sojojin da suka yi juyin mulki za su taka a wurin mika mulkin.

Gwamnatin sabon shugaban kasar na riko mai jiran gado, na da kwanaki 40 ta shirya sabon zabe, to amma ganin irin rikicin dake faruwa a yankin arewaci, zai yi wuya a iya cika wannan waadi.