Najeriya: an kai hari a garin Banki

'Yan sanda suna biciken tsaro a Maidguri
Image caption 'Yan sanda suna biciken tsaro a Maidguri

Rahotanni daga garin Banki dake kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Kamaru a jihar Bornon Najeriyar, na cewa wasu sun kai hare-haren bindiga da bama-bamai kan wasu cibiyoyi na hukumomin Nijeriya inda suka kashe jami'an tsaro da farar hula.

Maharan dai sun kai harin ne jiya da dare kuma mazauna garin sun bayyana cewa har zuwa asubahin yau ma sun yi ta jin karar harbe-harbe a garin.

Hukumomin tsaro sun tabbatar da kashe akalla mutane biyar da kuma kona wasu gine-ginen cibiyoyin tsaro bayan da aka yi amfani da abubuwa masu fashewa.

Hukumomi sun zargi kungiyar nan ta Boko Haram da kai hare-haren.