Sudan ta Kudu ta kwace mahakar mai ta Sudan

dakarun Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption dakarun Sudan ta Kudu

Sudan ta bayyana cewa, a yanzu filin hakar man ta mafi girma na Heglig na hannun dakarun Sudan ta Kudu.

Yaki a iyakar kasashen biyu ya sake barkewa ne a ranar Talata da rana.

Shugabannin kasashen duniya da dama sun bayyana fargabar su ta yiwuwar sake komawa yaki a tsakanin kasashen biyu, bayan wannan taho mu gama.

Yawanci dai ana ganin Heglig a matsayin yanki ne na Sudan, kodayake Sudan ta Kudu ta musanta haka.

Wakilin BBC ya ce yaki na baya bayan nan shine mafi kazancewa tun bayan da Sudan ta Kudu ta samu yancin kai a watan Yuli.

Karin bayani