Ghana ta soke kwangilar gidaje

gahan Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Shugaban Ghana John Attah Mills

Hukumomi a kasar Ghana sun bada sanarwar soke wata kwangila da suka baiwa wani kamfanin kasar Koriya ta gina gidaje dubu talatin ga jami'an tsaron kasar.

Ministan Ayyuka na Ghana Mista Mensah ya ce an soke kwangilar ce a sakamakon wasu matsaloli da suka dabaibaye ta.

A yanzu kenan kusan ta leko ta koma ga wasu jami'an tsaron kasar, wadanda suka fara murnar yuwuwar samun gidaje.

A karkashin yarjejeniyar dai aikin zai lakume dalar Amurka miliyon dubu guda da rabi, da gwamnatin Ghana za ta tsaya ma kamfanin wajen ciwo bashinsu.

Kampanin zai kuma gina wasu gidajen guda 200,000 a wasu sassan kasar daban daban.

Tuni dai 'yan adawa suka fara tsokaci kan lamarin tare da cewa dama sunyi ma gwamnati kashedi to amma ta ki ji.

A cikin watan Janerun bara ne dai shugaba John Atta Mills ya aza harsashin gina gidajen a wani kasaitaccen biki da aka gudanar a nan Accra.

Karin bayani