An rantsar da shugaban rikon kwarya a Mali

 Diouncounda Traore Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban rikon kwaryar Mali, Diouncounda Traore

An rantsar da Diouncounda Traore a matsayin shugaban riko na kasar Mali, a kokarin da ake na mayar da kasar bisa tafarkin demokradiyya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Maris.

Bayan ya rantse cewa zai mutunta tsarin mulkin kasar da kuma kare demokradiyya, Shugaba Diouncounda Traore ya kuma yi gargadin cewa, zai yi amfani da karfin soja wajen kwato yankin arewacin Malin da ya balle.

Mutane sun tashi tsaye don girmamawa, a yayin da jagoran wadanda suka yi juyin mulkin Kaptain Ahmodou Sanogo ke gaisawa da shugaban rikon kwaryar Mali, Diouncounda Traore, wanda ke alamta komawa ga mulkin farar hula.

Shi dai shugaban rikon kwaryar zai jagoranci wata gwamnati ne da ke da alhakin shirya zaben shugaban kasa cikin kwanaki 40.

Sai dai abun dubawa shi ne yiwuwar iya gudanar da zaben cikin wannan wa'adi, musamman idan aka yi la'akari da cewa tuni 'yantawaye suka rabe arewacin kasar daga sauran sassanta.

Bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin shugaba Toumani Toure ne dai, Abzinawa da 'yan gwagwarmayar Musulunci suka mamaye yankin arewacin kasar mai fadin gaske.

Karin bayani