Shugaba Goodluck ya sa hannu kan kasafin kudi

Shugaba Jonathan na Nijeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Jonathan na Nijeriya

A yau ne shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya rattaba hannu a kan kasafin kudin kasar na bana, inda ya amince da kusan dukkan sauye-sauyen da Majalisun dokokin kasar suka yi a watan da ya gabata.

Shugaba Jonathan ya ce kudaden da za a kashe sun kai dala biliyan 30 - watau kusan naira tiriliyan hudu da biliyan dari bakwai.

Za a gudanar da kasafin kudin ne akan dala 72 kan kowace gangar mai, sabanin dala 70 da shugaban ya gabatar tun farko.

Da yake sanya hannu a kan kasafin kudin, shugaba Goodluck Jonathan ya ce an tsara kasafin na bana ne domin cigaban tattalin arzikin kasar da samar da ayyukan yi.

Sai dai kasafin na bana ya nuna cewa kudaden da aka ware domin ayyukan ci gaban kasa da kadan suka haura kashi daya cikin hudu na kasafin kudin, abinda ke nuna cewa har yanzu ba ta sauya zani ba - a tsarin kasar na kashe mafi akasarin kudaden shigar da take samu daga man fetur, kan tafiyar da ayyukan gwamnati.

Karin bayani