Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Guinea Bissau

Guinea Bissau
Image caption Guinea Bissau

Kungiyar raya tattalin arzikin Afrika ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO ta yi Allah wadai da abin da ta bayyana a matsayin yunkurin juyin mulkin da aka yi a Guinea Bissau.

Rahotanni dai na nuna cewa an jiyo karar harbe-harbe a kusa da gidan tsohon Fryan Ministan kasar Carlos Gomes Junior.

Izuwa yanzu dai ba a san inda Mr Gomes Junior yake ba, wanda ke kan gaba a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar wanda za a yi a ranar 22 ga wannan wata na Afrilu, bayan da abokin adawar sa Kumba Yala ya janye daga takarar.

Shi dai Mr Yala ya janye daga takarar ne, saboda zargin da ya yi cewa an tabka magudi a zagayen farko.

Guinea-Bissau na da tarihin juyin mulki, inda yunkuri na baya bayan nan shi ne na watan Decembar bara.

Karin bayani