Za a fara tallata mukaman gwamnati a Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jonathan ya yi alkawarin kawo sauye-sauye

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya umarci ministocin kudi da na lafiya na kasar da su tallata mukaman shugabannin Hukumar tattara kudaden shiga (FIRS) da Hukumar Insorar lafiya NHIS domin cike guraben da wadanda suka cancanta.

Jonathan ya bayar da umarnin ne lokacin da yake bayar da lambar yabo ga wadanda suka lashe kyautar shirin "You Win Programme" a Abuja.

Shugaban ya ce daga yanzu za a rinka tallata dukkan mukaman gwamnatin tarayya domin baiwa 'yan Najeriyar da suka cancanta damar dare wa kan mukaman maimakon a nada wadanda aka ga dama.

Ya ce daga yanzu, dukkan muhimman mukaman gwamnatin Najeriya za a rinka nada su ne ta hanyar la'akari da kwarewa, yana mai cewa batun ubangida ya zama tarihi.

"Mun yanke shawarar cewa wasu daga cikin wadannan mukaman na siyasa za a rinka tallata su ga 'yan Najeriya baki daya, kuma za mu dauki wadanda suka fi kwarewa.

"A 'yan kwanakin nan mun so mu nada sabbin manyan daraktoci domin su jagoranci Asusu na musamman na "Sovereign Wealth Fund" kuma mun tallata su ga 'yan Najeriya. Ba ka bukatar ka san shugaban kasa kafin ka samu aiki matukar dai ka cancanta".

Jonathan ya ce nan bada jimawa za a tallata mukaman babban sakataren Hukumar Insorar lafiya NHIS da kuma shugaban Hukumar tattara kudaden shiga FIRS domin samun wadanda suka cancanta.

Karin bayani