Kumbon Korea ta Arewa ya rikito bayan harbawa

Korea ta Arewa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta tabbatar da cewa yunkurinta na harba tauraron dan-Adam sararin samaniya bai yi nasara ba.

Korea ta Arewar dai ta tabbatar da rahotannin da Amurka da wadansu kasashe suka fitar ne cewa yunkurin na ta ya gaza yin nasara.

Korea ta Kudu da Japan sun ce tauraron ya fashe bayan minti daya ko biyu da harba shi, kuma ya tarwatse, kimanin kilomita 150 daga gabar tekun Korea.

Kakakin gwamnatin Amurka ya bayyana harba tauraron da cewa wata takalar fada ce; hakazalika Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira wani taron gaggawa wanda za a gudanar ranar Juma'a don tattaunawa a kan batun.