Bama-bamai sun fashe kusa da ofishn jakadancin Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Obama a Colombiya

Wasu kananan bama- bamai guda biyu sun fashe a babban birnin Kasar Colombia na Bogota, kusa da ofishin jakadancin Kasar Amurka.

Babu dai wanda ya jikkata sakamakon fashewar bama- baman.

Lamarin ya auku, bayan saukar Shugaba Obama a cikin Kasar domin halartar wani taro.

'Yan sanda sunce wani dan karamin bam har ila yau ya sake fashewa a garin da za ai taron.

An dai tusa keyar jami'an tsaron da hukumar leken asirin Amurkan ta tura Colombian domin kare Shugaba Obaman zuwa gida, bayan da aka zarge su da nuna rashin da'a.

Karin bayani