Iran na ganawa da kasashen yamma akan shirin nukiliyarta

Hakkin mallakar hoto AFP

Jami'an diplomasiyya na kasashen yamma da ke halartar taro a kan shirin Iran na nukiliya, sun ce an fara tattaunawar da kafar dama.

Suka ce, da alama tawagar kasar Iran a shirye take ta saurari kokensu.

A cewar wani jami'in yammacin duniyar, yanayin tattaunawar ya sha bamban sosai da na ganawar da bangarorin biyu suka yi a shekarar da ta wuce.

Iran dai ta musanta cewa, tana kokari ne ta kera makaman nukiliya.

Taron na yau a birnin Santambul na Turkiyya, ya hada masu sasantawa na bangaren Iran, da kuma wakilai daga Amurka, Rasha, China, Burtaniya, Faransa da kuma Jamus.

Tattaunawar dai na zuwa ne yayinda ake fargabar cewa watakila Israila ta kai hari akan wuraren ayyukan Nukiliyar Iran din.

Shugaba Barrack Obama ya bayyana tattaunawar da cewa wata dama ce ta karshe da ake da ita don kawo karshen takaddamar da ake yi akan shirin nukiliyar Iran din ta hanyar Diplomasiyya.

Karin bayani