Manyan Kasashen Duniya za su gana da Iran

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption shugaban iran Ahmadinejad

Manyan Kasashen duniya za su gana da Kasar Iran a karo na farko a fiye da shekara guda yau asabar, domin tattauna aikace aikacen nukiliyar Kasar Iran.

Kasashen Amurka da Rasha da China da Birtaniya da Jamus za su tattauna da masu shiga tsakani na kasar Iran din a birnin Istanbul.

Shugaba Obama yace tattaunawar, ita ce ta karshe.

Amurkan dai na zargin Iran da kokarin kera makaman nukiliya, zargin da Iran din ta sha musantawa.

Karin bayani