Sudan ta kudu ta ce Sudan ta kashe mata mutane biyar

Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumomin Sudan ta kudu sun zargi dakarun Sudan da yin ruwan bama-bamai a wata kasuwa inda suka hallaka mutane a kalla biyar.

An kai harin ne a kusa da garin Bentiu a Sudan ta kudu.

Kawo yanzu dai Khartoum bata maida martani ba akan harin.

Tun farko Sudan ta kudun ta ce ta Sudan ta kudun ta ce, ta fatattaki sojojin kasar Sudan, wadanda suka kai hari kusa da yankin Heglig mai arzikin mai, wanda dakarun Sudan ta Kudun suka kwace a ranar Talatar da ta gabata.

Mataimakin shugaban Sudan ta Kudun Riek Machar ya ce a jiya an yi gumurzu a wani yanki mai nisan kimanin kilomita ashirin da biyar, a arewacin rijiyar man Heglig.