Majalisar dinkin duniya na shirin tura tawaga Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption masu kin gwamnatin Assad

Mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin duniya sun kammala shawara kan wani daftari na samarda wata tawwagar sa- ido, da zata tafi zuwa kasar Syria, domin ta duba yadda shirin tsagaita wuta ke gudana.

Ana tsammanin a yau asabar mambobin zasu kada kuri'a kan sabon daftarin a birnin New York.

Mai magana da yawun wakilin Majalisar dinkin duniyar Kofi Anan, yace 'yan tawwagar sun shirya tsaf domin hawa jirgi zuwa Syrian, da zarar an amince da shawarar.