Majalisar Dinkin Duniya zata tura masu sa ido a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption masu kin gwamnatin Assad

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yanke shawarar tura wata tawaga don ganin yadda yarjejeniyar tsagaita bude wuta ke aiki a tsakanin gwamnati da 'yan adawa a kasar.

Kwamitin ya kuma yi Allawadai da yadda dakarun gwamnati ke cin zarafin bil'adama kasar.

Wa'adin tsagaita bude wuta a kasar dai na fuskanatr barazana bayan da aka ruwaito cewa dakarun gwamnati sun hallaka mutane goma sha bakwai a wani harin roka a birnin Homs.

Amurka ta ce wannan sabon fadan ya sa alamar tambaya akan ikrarin Syria na cewa tana so a kawo karshen zubda jinin da ake yi a kasar