Fursunoni kusan 400 sun tsere a Pakistan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption sojojin Pakistan

Kusan Fursunoni dari hudu ne suka tsere daga wani gidan yari dake arewa maso yammacin Kasar Pakistan, bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari kan gidan yarin

'Yan Sanda sunce 'yan bindigar sunzo ne cikin kananan motoci da kuma manya, inda sukai amfani da bindigogi da kuma gurneti wajen kaddamar da hari akan gidan yarin

Lamarin dai ya auku ne a garin Bannu kusa da kan iyakar Afghanistan

Cikin wadanda suka tsere daga gidan yarin dai, sun hada da 'yan bindigar su kansu

Mayakan Taliban dake Pakistan, sunce su suka kaddamar da harin

Karin bayani