Shugaba Zuma zai yi amarya

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma, wanda da ma yana da mata ukku, zai yi amarya.

Wani kakakin fadar shugaban ya tabbatar cewa, Jacob Zuman, wanda a kwanan nan ya yi bikin cika shekaru saba'in da haihuwa, zai kuma zama ango a karshen makon gobe.

Za a yi bikin ne a kebe.

Shekaru da dama kenan da shugaba Zuman, da kuma amaryar tasa, Bongi Ngema, suka yi auren gargajiya.

Shekaru biyu da suka wuce ne ya auri matarsa ta ukku.