Sojoji a Guinea Biassau za su kafa majalisa

Hakkin mallakar hoto INTERNET
Image caption Sojojin Guinea Bissau

Sojojin da suka kwace mulki a Kasar Guinea Bissau, sunce zasu kafa majalisar wucin gadi ta kasa, tare da shugabannin 'yan adawa

Mai magana da yawun sojojin yace za a rusa majalisar dokoki, za kuma a nada shugabankasa na rikon kwarya da kuma Firayim Minista.

An dai jikkata mutane da dama a lokacin da sojoji suka tarwatsa wani gangami da masu zanga- zanga suka shirya, inda suke kiran a saki Firayim Ministan Kasar Carlos Junior, wanda aka tsare a lokacin juyin mulkin na ranar Alhamis

Ana dai tunanin cewar an kai Mr. Junior zuwa wani barikin sojoji dake Bissau.

Karin bayani