An yi hatsanaiya wurin shari'ar Ibori a London

James Ibori a hannun hagu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption James Ibori a hannun hagu

A yau ne wata kotu a nan Landan ta dakatar da fara zama domin yanke hukunci kan laifuffukan a ake zargin tsohon gwamnan jihar Delta ta Najeriya, sakamakon wani kutse da hatsaniya da magoya bayan tsohon gwamnan suka yi a kotun.

Wasu da suka shaida lamarin na cewa magoya bayan tsohon gwmnan jihar Delta mai arzikin man fetur a Najeriya, sun barke da ihu ne bayan an hana su shiga cikin kotun.

Ana tuhumar James Ibori ne da laifin azurta kai da dukiyar al'umma na kimanin dalar Amurka miliyan dari biyu da hamsin.

Kazalika tsohon gwamnan ya mallaki jirgin sama na hawa, da ya saya kan dalar Amurka miliyan ashirin tare da wadansu manyan motoci na kasaita masu sulke, tare da kashe makudan kudade a makarantu, da otel-otel na isa a kasashen waje.

A gobe Talata ne ake sa ran za a yanke ma James Ibori dan shekara 49, hukunci.

Karin bayani