An yanke wa Ibori daurin shekaru 13 a gidan kaso

 James Ibori
Image caption James Ibori ya taba zama daya daga cikin mafiya fada aji a jam'iyyar PDP

Wata kotu a London ta yankewa tsohon gwamnan jihar Delta a Najeriya James Ibori, hukuncin daurin shekaru 13 a gidan kaso kan zargin cin hanci da halatta kudaden haram.

James Ibori ya amsa laifin zamba da halatta kudaden haram a wata kotun birnin London a watan Fabreru.

An zarge shi da sace dala miliyan 250 daga lalitar gwamnati sannan ya tura kudaden zuwa wasu bankuna a Ingila domin gudanar da rayuwar kasaita ciki har da mallakar jirgin sama da manyan motoci.

Laifin da ya amsa ya samo asali ne da wani bincike da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ta fara a 2005.

Yana da kariya daga shari'a a lokacin mulkinsa daga shekarun 1999 zuwa 2007.

Dukka laifukan ya aikata su ne a shekaru takwas din da ya yi yana mulkar jihar ta Delta.

Wata kotu a Najeriya ta wanke shi daga dukkan laifukan da ake zarginsa da aikatawa, a wata shari'a da ake ganin na da alaka da siyasa, ganin yadda yake da alaka da marigayi shugaban Najeriya Umaru Musa 'Yar'adua.

Karin bayani