Taliban na artabu da sojin Afghanistan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hayaki kusa da majalisar dokokin Afghanistan

Karar Harbin bindigogi da fashewar bama- bamai, sun girgiza babban birnin Kasar Afghanistan na Kabul a rana ta biyu, a yayinda jami'an tsaro ke kokarin kawo karshen aikace- aikacen mayakan Taliban

Wani wakilin BBC yace jami'an tsaro suna bi daki- daki domin duba masu tada kayar bayan da suka mutu, da kuma makaman da aka boye

Ana kuma samun rahotannin karar harbin bindigogi kusa da majalisar dokokin Kasar, inda 'yan bindigar sukai garkuwa da wasu ma'aikata magina su tara a wani gida

An kuma kaiwa Sansanin NATO da ofisoshin jakadancin kasahen yammacin duniya hari a ranar asabar.

Karin bayani