Sudan ta kaiwa Sudan ta kudu hari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption sojin 'yanta Sudan

Majalisar dinkin duniya ta tabbatar da cewa an kai harin bam akan Sudan ta Kudu.

Tace wasu kananan jiragen Sudan biyu ne suka watso bama- bamai guda hudu akan garin Bentu, kuma mutum guda ya rasa ransa.

Hukumomin garin sunce wani jirgin Sudan ya kuma yi aman wuta akan garin Mayom, inda mata da kananan yara suka rasa rayukansu.

A ranar lahadi dai, wata kungiyar 'yan tawaye dake Sudan ta Kudu ta gaza samun nasara a yunkurin da tayi na kwace kauyen Kuek dake jahar Upper Nile.

Sudan ta Kudu dai ta zargi sojojin Sudan da samar da makaman Atilare ga 'yan tawaye.

Karin bayani