Za a bayyana takardun sirri na Burtaniya

David Cameron Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Firayim Minista David Cameron na Burtaniya

Nan gaba kadan za a fitar da wadansu bayanan tarihi wadanda suka nuna cewa ministocin Burtaniya suna sane da cin zarafi har ma da kisan mutanen da aka rika yi a shekarun karshe na daular Burtaniyar.

Takardun sun bayar da cikakken bayanin yadda Burtaniyar ta yi da 'yan tawaye na Mau Mau a kasar Kenya da masu ra'ayin kwaminisanci wadanda suka tayar da kayar-baya a Malaya a shekarun 1950.

A wani kaulin, a Kenya, bayanan sun nuna yadda aka kone wani mutum wanda ake zargi da ransa.

Wani bayanin kuma ya nuna cewa mahaifin Shugaba Barack Obama na Amurka yana cikin wadanda Burtaniyar ke sa ido a kansu a cikin daliban kasarKenyadake karatu a Amurka.