Sabon tashin hankali ya barke a kasar Masar

'Yan kungiyar Brotherhood Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kungiyar Muslim Brotherhood suna zanga-zanga a Masar

Tashin hankali ya barke a Masar sakamakon haramcin da hukumar zaben kasar ta dora a kan wadansu ’yan takarar shugabancin kasar.

A cikin wadanda aka haramtawa tsayawa har da 'yan takara biyu na kan gaba masu kishin Islama da kuma tsohon jagoran hukumar leken asiri ta kasar, Umar Suleiman.

Da maraicen ranar Talata ne magoya bayan dan takarar shugabancin kasa na masu tsatstsauran ra'ayin addinin Islama, Hazim Salah Abu Isma'il, suka yi fito-na-fito da jami'an tsaron da aka dorawa alhakin kare ofishin hukumar zaben.

Magoya bayan dan takarar sun hallara a ofishin hukumar ne inda suka rika jifa da takalmansu bayan da hukumar ta bayyana haramci na dindindin a kan ’yan takara goma, ciki har da Abu Isma'il.

Shi dai Abu Isma'il ya shaidawa magoya bayansa cewa shawarar haramta masa takarar wani makirci aka kulla kuma cin amanar kasa ce.

Jim kadan bayan hukumar ta bayar da sanarwar, Abu Isma'il ya yi kira da a tattauna a bainar jama'a don ya nuna rashin jin dadinsa da matakin, ya kuma yi yunkurin shiga cikin ginin ofishin hukumar amma jami'an tsaro suka hana shi.

Dan takarar ya kuma zargi hukumar da amfani da takardun boge don nuna cewa mahaifiyarsa na da takardun zama 'yan kasar Amurka.

Daftarin Kundin Tsarin Mulkin kasar na watan Maris dai ya ce wajibi ne ’yan takara su kasance Misrawa kuma ’ya’yan Misrawa.

Ana dai daukar tsohon shugaban hukumar leken asiri Umar Suleiman, da dan takarar kungiyar Muslim Brotherhood Khairat al-Shatir, da ma Abu Isma'il, a matsayin 'yan takarar da ke gaba-gaba.

Yanzu dai ya zama tilas ga kungiyar Muslim Brotherhood, tun da ta rasa uwa a zaben shugaban kasar, ta yanke shawara a kan ko za ta yi uwar daki.

Sai dai kuma wannan al'amari na iya zama dama ga tauraruwar wadansu ’yan takarar ta haskaka.

Wadannan ’yan takara kuwa sun hada da tsohon Sakatare Janar na Kungiyar Kasashen Larabawa Amr Moussa, da kuma wani mai kishin Islama wanda ya bijirewa kungiyar Muslim Brotherhood.

Karin bayani