An haramtawa mutane goma tsayawa takara a Masar

Magoya bayan Omar Suleman Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Magoya bayan Umar Suleman

Kamfanin dillancin labarai na kasar Masar yace, anyi watsi da daukaka karar wasu mutane goma da suke son tsayawa takarar shugabancin kasar, amma aka haramta musu.

Daga cikin mutanen da lamarin ya shafa dai har da na gaba-gaba a neman takarar, wadanda suka hada da tsohon babban jami'in leken asiri a lokacin mulkin Hosni Mubarak, Omar Sulaiman, da dan takarar kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, Khairat Al Shater, da kuma malamin nan mai kaifin kishin Islama, Hazem Salah Abu Isma'il.

A watan gobe ne za a yi zaben shugaban kasar, wanda muhimmin mataki ne a tafiyar siyasar kasar, bayan an kawar da shugaba Hosni Mubarak.

Karin bayani