An amince da yarjajeniyar wucin-gadi a Syria

Rikicin kasar Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Har yanzu rikicin Syria yaki-ci-yaki-cinyewa

Syria da Majalisar Dinkin Duniya sun sa hannu kan wata yarjajeniyar wucin-gadi, wadda ta zayyana ka'idojin tura tawagar sa-ido ta majalisar a kasar Syriar.

Wata sanarwa daga ofishin mai shiga tsakani a rikicin, Kofi Annan, ta ce yana kuma tattaunawa da wakilan kungiyoyin adawar Syriar.

Kawo yanzu, wata karamar tawagar masu sa-ido ta Majalisar Dinkin Duniya ce ke kula da lamurra a Syriar, inda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula.

Sai dai ba'a san hakikanin irin 'yancin da za a baiwa masu sa ido domin shiga cikin wuraren da wannan lamari ya shafa ba.

Ya zuwa yanzu dai ba'a basu damar shiga cikin wurin da rikicin ya fi zafi ba watau birnin homs inda ake ci gaba da yiwa wuraren da 'yan tawaye keda iko lugaden wuta.

Rasha na da ra'ayi daban

Sakatare janar na Majlisar Dinkin Duniya Ban ki Moon ya ce janyewar manyan makamai da tankunan yaki wani abu ne mai matukar muhimanci.

Sai dai jakadan kungiyar kasahen Larabawa a kasar Turkiya Mohammed Al Fateh Al Nasrey, ya ce kalaman da suka fito daga Majalisar Dinkin Duniya na bukatar a dauki kwararan matakai:

"Muna goyon bayan sanarwar da sakatare Janarar Ban kin Moon ya fitar dari bisa bisa dari. Amma ya kamata a aiwatar da matakai masu tsauri kan wannan gwamnati domin taka mata birki wanda zai kawo karshen murkushe 'yan adawa".

Sai dai Rasha nada ra'ayi iri daya da ta gwamnatin Syria akan cewa 'yan tawaye da ke rike da makamai sune suke ruruta tashen-tashen hankulan da ake fuskanta yanzu.

Karin bayani