Rayuwar siyasar Charles Taylor

Charles Taylor Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mr Taylor ya yi kaurin suna a nahiyar Afrika da ma duniya baki daya

Charles Taylor ya fara shiga harkokin siyasa a shekarar 1980 a lokacin da ya ziyarci Liberia a matsayin jagoran kungiyar 'Yan Liberia mazauna kasar Amurka. Bayan juyin mulkin sojoji ne kuma ya samu aiki a gwamnatin Samuel Doe.

An kara masa mukami zuwa mataimakin ministan cinikayya a gwamnatin Doe. Mr. Taylor ya bar Liberia, inda ya koma Amurka bayan an zarge shi da wawure kusan sama da dala miliyan daya.

Kuma yayin da yake zaman gidan kaso a Amurka ya tsere daga kurkukun a wani yanayin da har yanzu ake takaddama akai.

Daga bisani kuma Mr. Taylor ya kafa kungiyar sa ta 'yan tawaye mai suna National Patriotic Front of Liberia wacce ta kaiga tumbuke gwamnatin Samuel Doe.

Hira da kafafen yada labarai

Karfin kwarjinin da Charles Taylor ke da shi ya kan sanya masu sukarsa su koma suna goyon bayansa. Ga misali lokacin da ya je Monrovia babban birnin Liberia a shekarar 1995 dubun dubatan mutanen da a baya sukayi ta sukarsa ne kuma suka fito tarbarsa suna yaba masa.

Charles Taylor ya rike ragamar shugabancin Liberia daga shekarar 1997 zuwa shekarar 2003 a lokacin da yayi murabus bayan da ya fuskanci matsin lamba daga kasashen duniya don sauka daga mulkin kasar.

Kodayake a hukumance ya nada jami'ai masu bashi shawarwari, amma a zahiri 'yan jeka na yika ne don baya saurarensu.

Wani mai taimaka masa da ya bukaci a boye sunansa ya taba shaidawa wakilin BBC a Liberia cewa, da ya saurari masu bashi shawara, da bai tsinci kansa cikin halin da yake ba.

Yana daukar kansa kamar masarauci a karni na goma sha tara, wanda ke yin alfarma ga mabukata tare da masaniyar cewa za 'a yaba masa kuma a taimaka masa a saboda hakan.

Haka kuma yana da masaniyar karfin da kafafen yada labarai ke da shi, ya kuma san yadda zaibi da su don yi masa abinda yake so.

A tsawon shekarun 1990, ya yi wasu hirarraki masu kama da wasan kwaikwayo ta wayar tarho da shirin Turanci na BBC Focus on Africa.

Da fari ya yi magana a matsayin madugun 'yan tawayen da ba'a sanshi sosai ba, inda ya sanar da cewa zai mamaye Liberia.

A wata fitacciyar hirar kuma a 'yan shekarun da suka wuce, a yayin da editan ya yi nuni da cewa wasu na yi masa kallon wanda bashi da banbanci da mai kashe mutane, sai ya daga muryarsa ya ce " Annabi Isa ma an zarge shi da kashe mutane a lokacin rayuwarsa".

Karin bayani