'Yan arewa sun kalubalanci Goodluck Jonathan

Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Wata kungiya ta wadansu 'yan arewacin Najeriya wadanda ke kiran kansu da suna Concerned Northerners ta fitar da wata sanarwa tana mai cewa za ta shiga cikin karar da wani dan jam'iyyar PDP, Mista Cyriacus Njoku, ya shigar yana neman kotu ta hana Shugaban kasar Goodluck Jonathan sake tsayawa takarar shugabancin kasar.

A farkon makon nan ne dai shugaban kasar, lokacin da yake mayar da martani ta bakin lauyansa a kan karar, ya ce yana kan wa'adin mulkinsa ne na farko, ba karo na biyu ba kamar yadda wanda ya shigar da karar ke da’awa.

Sanarwar, wacce mutanen da suka jagoranci taron da kungiyar ta yi, Dokta Junaidu Muhammad da Farfesa Auwalu Yadudu, suka sanyawa hannu, ta ce batun cewa ko wannan shi ne karo na farko ko na biyu da Shugaba Jonathan ke mulki batu ne da ya shafi kundin tsarin mulki, wanda kotu ce kadai za ta warware.

Don haka kungiyar ta yi kira ga Shugaba Jonathan ya kyale kotu ta yi aikinta ba tare da yayata maganar ta kafafen watsa labarai ba.

Sanarwar ta kuma ambato yadda wadansu na kusa da shugaban kasar ke yunkurin aiki da shawarwarin kwamitin Mai Shari'a Alfa Balgore a kan gyaran al'amuran zabe, wanda ya bayar da shawarar a rika shekara bakwai falle daya.

A cewarsu alamu na nuna cewa Shugaba Jonathan na son fara cin moriyar tsarin bayan kammala wa'adinsa na yanzu.

Saboda haka ne kungiyar ta ce ta sha alwashin farkar da kungiyoyin fararen hula da ma sauran jama'a da su yunkura don ganin bukatar karin wa'adin mulkin ba ta kai ko ina ba.

Karin bayani