Akwai ruwa mai yawa a karkashin kasa a Afirka

Taswirar yankin Afirka mai kunshe da ruwan karkashin kasa
Image caption Taswirar yankin Afirka mai kunshe da ruwan karkashin kasa

Masana kimiyya sun ce akwai wadansu maka-makan duwatsu da ke da ruwa a karkashin kasa a nahiyar Afirka, wadanda ruwan da ke cikinsu ya ninka abin da ake samu a doron kasa har sau dari.

Wadansu masu bincike wadanda suka yi rubutu a mujallar muhalli ta Environmental Research Letters, sun zana wata sabuwar taswira wadda ta nuna yawan ruwan da ke kwance a gulbin karkashin kasa a nahiyar.

Fiye da mutane miliyan dari uku ne dai ba sa samun tsaftattacen ruwan sha a fadin nahiyar ta Afirka; amma masanan na cewa maka-makan gulaben na karkashin kasa za su iya samar da wadataccen ruwan sha da na noma ga daukacin nahiyar.

Wannan ne dai karo na farko da masanan suka zayyana taswirar da ke nuni da wuraren da ruwan ya ke.

A cewar masanan da suka yi binciken ruwan yana da dimbin yawa, musamman ma a arewacin nahiyar.

Helen Bonsor na cikin masanan da suka gudanar da binciken, ta kuma shaidawa BBC cewa: “A arewacin Afirka ne wannan ruwa na karkashin kasa ya fi yawa a karkashin wadansu duwatsu a Algeria da Libya da Chadi.

“Yawan ruwan da wannan gulbin ya kunsa ya kai tsawon mita saba’in da biyar”.

Sai dai kuma kaiwa ga wannan ruwa ba abu ne mai sauki ba.

Masanan sun yi gargadin cewa gina manyan rijiyoyin burtsatse ba zai wadatar ba, kuma mai yiwuwa ya jawo asarar ruwan da ya shafe dubban shekaru a kwance a karkashin kasa.

Shawararsu ita ce yin amfani da kananan na'urorin zuko ruwa wadanda za a iya sarrafa su a wurare da dama.

Sun kuma ce ruwan na karkashin kasa ka iya zama kandagarki ga sauyin yanayi, suna masu kiyasin cewa ko da a wuraren da ke da matukar kamfan ruwa a nahiyar Afirka, akwai ruwan karkashin kasa wanda za a iya shekaru saba'in ana amfani da shi.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar dake nuna yawan ruwan dake karkashin kasa a Afrika

Karin bayani