2015: Kotu ta dage kara akan Shugaba Jonathan

jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Kasa da shekara guda tun bayan zaben shugaban Najeriya, tuni an fara ja-in-ja game da takarar shugabancin kasar ta shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.

Wata babbar kotun Abuja ta saurari wata kara, inda ake kokarin hana shugaba Goodluck Jonathan sake yin takara, nan da shekaru ukku masu zuwa.

Wani dan jam'iyar PDP mai mulkin ce, Cyriacus Njoku ya shigar da karar, yana neman kotu ta hana Dokta Goodluck Jonathan din yin takarar.

A ranar talatin ga watan Mayu mai zuwa ne za a koma kan shari'ar.

'Tunanin Zaben 2015'

Ko da yake dai akwai sauran lokaci, amma kuma gangar siyasa ta soma kadawa a duk fadin Najeriya akan wani abu da ake gani tamkar yinkuri ne ga shugaba Goodluck Jonathan ya sake neman tsayawa takara.

Batun ko shugaba Jonathan zai iya tsayawa takara ko kuma a'a, shine a halin yanzu ya kankane siyasar kasar inda aka soma zazzafar mahawara.

Wani dan jamiyyar PDP Cyriacus Njoku a yanzu haka dai shine ya kai kara zuwa wata babbar kotu a Abuja don hana Mista Jonathan tsayawa takara.

Kamar yadda Njoku ya bayyana, shugaba Jonathan na wa'adin mulkinsa na biyu ne, saboda yasha rantsuwar mukamin shugaban Najeriya har sau biyu. Sai dai kuma bangaren shugaban kasar na cewar a yanzu ne ya soma wa'adin mulkinsa na farko.

Ko da yake dai 'yan kudu sun soma kira-kirayen cewar ya sake tsayawa takara, kawo yanzu dai Mistan Jonathan yayi gum da bakinsa.

Abinda kuma ya janyo 'yan siyasa daga arewacin kasar a yanzu haka sun soma shiga damuwa akan batun shugabancin kasar.

A bara ne dai shugaba Jonathan ya bukaci a maida wa'adin mulkin shugabancin kasar ya koma wa'adi guda na shekaru bakwai, inda ya karyata cewar yana kokarin cigaba da zama kan kujerar shugabancin kasar ne irin salon yadda Abdoulaye Wade yayi a Senegal.

Goodluck Jonathan dai ya tsinci kansa akan mulki ne bisa kaddara sakamakon rasuwar Alhaji Umar Musa Yaradua a shekara ta 2010, inda ya kara sa wa'adin mulkin da ya ragewa margayin na shekara guda sannan kuma ya lashe zabe a bara.

Sai dai kuma da dama 'yan siyasa a Arewacin kasar na gannin cewar Mista Jonathan ya saba yarjejeniyar da aka kulla na raba mulki tsakanin kudu da arewacin kasar. Abinda kuma hakan ke nufi shine tsuggune bata kare ba.

Karin bayani