India ta yi gwajin makami mai dogon zango

Makami mai linzamin da India ta gwada Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Makami mai linzamin da India ta gwada, Agni 5

India ta yi gwajin wani kumbon makami mai linzami mai cin dogon zango, wanda zai iya daukar makamin nukiliya.

Wannan makami dai zai baiwa kasar ta India damar kai hari a kan wadansu manyan birane na China kamar su Beijing da Shanghai.

Da sanyin safiyar ranar Alhamis ne dai a agogon India aka harba makamin daga wani tsibiri wanda ke daura da gabar tekun kasar ta gabas.

Majiyoyin tsaro a kasar ta India sun ce an samu nasarar harba kumbon mai suna Agni 5, sai dai kuma ba tabbas a kan ko ya ya cimma tafiyar kilomita dari biyar kamar yadda aka yi fata.

Ba a harba makamin ba sai da jami'ai suka tabbatar da cewa yanayi ya inganta; don haka baya ga gwaji, wannan wata alama ce da ke nunawa masu adawa da India cewa wuyanta ya yi kauri.

Jami'an kasar sun musanta cewa don murza-gashin-baki suka yi gwajin, amma jama'a da dama sun yi amanna cewa manufarsa ita ce yin muzurai ga China.

In har aka tabbatar da cewa gwajin ya yi nasara, to India za ta shiga jerin wadansu tsirarun kasashe wanda a yanzu suka hada da mambobin Kwamitin Sulhu su biyar kawai.

Karin bayani