Shugaba Jonathan na cikin masu fada-a-ji a duniya

Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Mujallar Time ta kasar Amurka mai fitowa mako-mako ta sanya Shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, a cikin mutane dari da suka fi kowa karfin fada-a-ji a duniya.

Najeriya dai na cikin manyan kasashen duniya masu samar da danyen man fetur kuma daya daga cikin kasashen da suka fi albarkatun kasa.

Hasali ma ita ake wa kirari da giwar Nahiyar Afirka saboda tasirinta a harkokin yankin da kuma kasaitarta ta fuskar yawan jama’a.

Goodluck Ebele Jonathan kuma shi ne yake shugabantar kasar tun kimanin shekaru biyu da suka gabata; wadansu kuma na ganin tasirin kasar ka iya kasancewa ma’aunin tasirin shugaban nata a harkokin kasashen duniya.

Sai dai kuma yayin da wadansu ’yan Najeriya ke ganin ya cancanci shiga cikin wadannan mutane dari, wadansu gani suke yi ba shi da karfin fada-a-aji a kasarsa ma balle a duniya.

Malam Garba Muhammd wani dan Nijeriya ne kuma a ganinsa matsayin Shugaban ya kai na fada-a-ji a duniya don haka sakamakon zaben na mujallar Time bai bashi mamaki ba domin shugaban ya cancanta.

Amma kuma wadansu, irin su Malam Babangida Ahmed Gombe, suna yiwa Shugaba Goodluck Jonathan kallon shugaba mai rauni ainun wanda kuma ba ya iya yin kazar-kazar, hatta a harkokin kasarsa, wacce yanzu haka ke fama da matsaloli da dama da shugaban ya kasa amfani da karfin nasa na fada aji indai ya na da shi, wajen shawokanmatsalolin.

Ita dai mujallar Time din ta kasar Amurka ta kan ji ra’ayoyin mutane ne a sassa daban-daban na duniya a kan mashahuran mutanen da suke jin sun fi kowa karfin fada-a-ji a duniya, kuma mutanen da a kan zaba su kan fito ne daga fagage daban-daban na rayuwa kama daga na siyasa zuwa na kimiyya, da harkar shakatawa da tattalin arzki da dai sauransu.

Tuni dai Shugaba Goodluck Jonathan ya mayar da martani ga labarin kasancewarsa daya daga cikin mutane dari masu karfin fada-a-ji a duniya, yana godiya ga ’yan Najeriya da ’yan kasashen wajen da suka zabe shi kana ya jinjinja wa Mujallar ta Time ta kasar Amurka.

Bisa ga dukkan alamu dai za a ci gaba da tafaka muhawara akanzaben na Shugaba Goodluck Jonathan da mujallar ta yi, musamman a Najeriya, idan aka yi la’akari da halin da Nijeriya ke ciki, inda wadansu kuma ka iya duba lamarin ta fuskar siyasar duniya da kuma tattalin arziki.

Karin bayani