'Yan China na durkusar da mu —'Yan kasuwar Kwari

Kaya a Kantin Kwari
Image caption Kaya a Kantin Kwari

’Yan kasuwa a kasuwar Kantin Kwari da ke Jihar Kano a arewacin Najeriya na kokawa da abin da suka kira kakagida da ’yan China ke yi a kasuwar, abin da suka ce yana durkusar da ’yan kasuwa ’yan kasa da dama.

Kasuwar ta Kantin Kwari dai na cikin manyan kasuwannin Jihar wadanda ke samun baki daga gida da ma wadansu kasashen nahiyar Afirka ta Yamma.

Kuma a iya cewa ita ce kasuwar da jihar ta fi alfahari da ita wajen girma da hadahadar daruruwan miliyoyin nairori a kowacce rana, gami da samar da ayyukan yi ga dubban jama'a.

Watakila wadannan damammaki da muhimmancin kasuwar da ’yan China suka kyalla ido suka gano su suka sanya su daukar matakan kawo kaya suna kasawa da kansu a kasuwar, a maimakon sayarwa da ’yan kasuwa a jimlace su ma su samu nasu rabon.

Alhaji Bashir Dan Baba na cikin daruruwan ’yan kasuwar da ke ganin mai doki na neman komawa kuturi.

A cewarsa, “Kasuwancinmu gaba daya ya tabarbare, za ka je yau ka sayo kayan [naira] miliyan goma amma ba za ka samu [naira] dubu hamsin ba a Kantin Kwari—akwai [shago] a Kantin Kwari [inda] bandir dai-dai ’yan China ke zama suna sayarwa”.

Daya daga cikin ’yan Najeriyar da ’yan kasuwar ta Kwari ke zargi da hada kai da ’yan China wajen zama ummul-haba'isin kwace kasuwanci daga 'yan gida ya kare kansa da cewa: “Shi wannan kanti a hakika ba na kowa ba ne, nawa ne na kai na; amma mun yi hadin gwiwa—su suna da dukiya ni ina da kanti—daga cikin kayan da ke cikin kantin wani ba’ari nawa ne, wani kuma nasu ne”.

Da dama daga cikin yan kasuwar dai na zargin Kungiyar ’Yan Kasuwar Kwari da baiwa ’yan China damar yin kakagida da cin karensu babu babbaka a kasuwar.

Sai dai a cewar shugaban Kungiyar, Alhaji Liti Kulkul, suna daukar matakan da doka ta tanada musu, amma fa yakin ya fi karfinsu.

“Mu kungiya ce, akwai gaba da mu—su ne gwamnati”, in ji Alhaji Liti.

Ya kuma kara da cewa, “Zuwanmu ne ake rufe kantin dan China ya yi sati biyu [ko] sati uku…. Amma a wannan magana hadin kai suke samu daga ’yan kasa: za ka je ka tambayi mutum ka ce ‘wannan kanti ba naka ba ne, na dan China ne, ya yi maka rantsuwa kantinsa ne’”.

Wakilin BBC ya yi yunkurin jin ta bakin gwamnatin Jihar Kano a kan cewa an sha kai mata korafi, amma ta nuna halin ko-in-kula, sai dai jami'an gwamnatin sun ce Kwamishinan Ciniki ne kadai ya kamata ya yi magana, shi kuma ba ya nan, wayarsa kuma tana kashe.

An dai jima ana kokawa da kama-wuri zauna da ’yan kasuwar China ke yi a al'amuran kasuwanci a Najeriya, musamman ma dai a Kantin Kwari, sai dai har yanzu babu wani mataki na a-zo-a-gani da hukumomi ke dauka na kare ’yan kasuwarsu daga hadarin da suke fuskanta na karbe musu al'amuran kasuwancin, gashi kuwa tuni ruwa ya cinye wadansu har iya wuya.