Wani Kwamandan Libya yayi karar Jack Straw

Abdulkarim Belhadj Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Abdulkarim Belhadj

Lauyoyin dake wakiltar wani kwamandan sojan Libya, Abdulkarim Belhadj za su shigar da tsohon sakataren hulda da kasashen wajen Birtaniya, Jack Straw kara a gaban kotu.

Kwamandan dai yana zargin Jack Straw ne da mika shi ga jami'an tsaron gwamnatin Kanar Gaddafi.

Abdulkarim Benhadj yace, hukumar leken asiri ta CIA ce ta cafke shi tare da iyalinsa cikin shekara ta 2004 a kan hanyarsu daga Birtaniya zuwa Malaysia:

Wakilin BBC yace: da maraicen jiya ne dai lauyoyin Abdulkarim Belhadj suka mikawa Jack Straw takardun sammaci.

Ya zuwa yanzu dai Jack Straw bai ce komai dangane da wannan batu ba.

Babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, Luis Moreno Ocampo ya isa Libya inda zai tattauna a kan makomar Saif Al Islam, dan marigayi Kanar Mu'ammar Gaddafi.

Ita dai gwamnatin rikon kwaryar Libya ta ki mika Saif Al Islam ga kotun dake birnin Hague inda ake tuhumarsa da laifin cin zarafin bil'adama.

Wani jami'in gwamnati da yake da masaniya a kan batun, yace, an kusa cimma matsaya ta yadda za a yiwa Saif Al Islam shari'a a cikin Libya, amma bisa sa idon kotun ta duniya:

Wakilin BBC yace, tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka soma korafin cewa, tsarin shari'a na Libya ba shi da karkon da zai iya gudanar da babbar shari'a kamar wacce za'a yiwa Saif Al Islam.

Karin bayani