Amurka da Faransa sun tsaurara matsayi kan Syria

Masu sa ido na Majalisar Dinkin Duniya a Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu sa ido na Majalisar Dinkin Duniya a Syria

Amurka da Faransa sun dauki matsaya ta ba-sani-ba-sabo a kan gwamnatin Syria yayin wani taro a Paris, inda kiris ya rage su bukaci a dauki matakan soji a kan kasar ta Syria.

Yayin taron kasashe masu goyon bayan 'yan adawar Syria wadanda ake yiwa lakabi da Abokan Syria, Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, ta yi kira ga daukacin kasashen duniya su kakabawa kasar ta Syria takunkumin hana sayar mata da makamai, idan gwamnatin Bashar al-Assad ta ci gaba da keta yarjejniyar tsagaita bude wuta.

Shi ma Ministan Harkokin Wajen Faransa, Alain Juppe, ya ce baya ga wannan, kasashen na kuma duba yiwuwar daukar wadansu matakan na dabam.

“Mun fito karara yayin bayyana irin aikin da ya kamata a yi [mun nuna cewa] a wajenmu abu mafi muhimmanci a yau shi ne aiwatar da shirin samar da zaman lafiya na Kofi Annan, wanda muke ganin dama ce ta karshe ta kaucewa yakin basasa a Syria”, in ji Mista Juppe.

Ministan na Faransa ya kuma kara da cewa don tabbatar da cewa an aiwatar da shirin, wajibi ne a girke tawagar masu sa ido a kasar ta Syria ba tare da bata lokaci ba, idan kuma kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu to lokaci ya yi ke nan da za a dauki wadansu matakan.

A halin da ake ciki kuma, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya bukaci Kwamitin Sulhu ya amince da wani shiri na fadada tawagar masu sa idon da za a aike Syria bayan gwamnatin kasar ta amince da hakan.

Sai dai kuma jami'ai a Majalisar ta Dinkin Duniya sun ce yana da muhimmanci a tuna cewa tawagar sa ido kawai za ta yi a kan tashe-tashen hankulan da ake yi ba magance su ba.

Karin bayani