Amurka ta soki sojojinta a Afghanistan

afghanistan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Amurka a Afghanistan

Amurka da kungiyar tsaro ta NATO sun yi Allah-wadai da wasu sojan Amukra da suka dauki hoto da gawar wani dan kunar bakin wake da tayi kaca-kaca a Afghanistan.

Amurka da NATO dai sun yi alkawarin gudanar da cikakken bincike akan lamarin.

Fadar White House ta bayyana abinda sojan suka yi a matsayin abin takaici, yayin da shi kuma sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO, Anders Figh Rasmussen yace, abinda sojan suka yi ba shi alaka da mufofin NATO a Afghanistan.

Jaridar Los Angeles Times ce ta wallafa hoton wanda wani sojan Amurka ya dauka a shekara ta 2010.

Ma'aikatar tsaron Amurka wato Pentagon ta nemi kada a wallafa hoton amma kuma sai jaridar ta buga.

Wannan ce matsala ta baya-bayannan da dakarun Amurka suka shiga a Afghanistan, bayan da akan dauki hoton wasu sojojin suna fitsari akan gawarwakin 'yan Afghanistan, da kuma kona Alkur'ani mai girma.

Karin bayani