BBC navigation

Sudan ta kudu za ta janye daga Heglig

An sabunta: 20 ga Aprilu, 2012 - An wallafa a 13:36 GMT
Dakarun Sudan ta Kudu a yankin Heglig

Dakarun Sudan ta Kudu a yankin Heglig


Gwamnatin Sudan ta Kudu ta umarci dakarun sojinta su janye ba tare da bata lokaci ba daga yankin Heglig wajen da suka kwace a hannun jamhuriyyar Sudan makon jiya.

Wata sanarwa da shugaba Salva Kiir ya fitar ta ce nan da kwana uku dakarun sojinsu za su kammala janyewa daga yankin.

Mamayar da sojojin su kayi ta sa an fara fargabar cewa kasashen biyu na iya fadawa yaki gadan-gadan.

An yi ta yin tur da mamayar da Sudan ta kudun ta yiwa Heglig, inda jamhuriyyar Sudan ke hakar mai.

Majalisar dinkin duniya da kungiyar tarayyar Afirka sun nemi janyewar sojojin ba tare da wani sharadi ba.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.