BBC navigation

Afghanistan ta ce ta cafke 'yan ta'adda

An sabunta: 21 ga Aprilu, 2012 - An wallafa a 14:51 GMT

Hukumar leken asirin Afghanistan ta ce ta cafke mutane biyar da tace sun yi shirin kai wani mummunan hari a Kabul babban birnin kasar a makon jiya.

Jami'a sunce ukku daga cikin mutanen 'yan Pakistan ne, kuma biyun 'yan Afghanistan ne.

Jami'an sun kuma ce an kama mutanen ne da wata tirela shake da nakiyoyi.

A cewar jami'an Afganistan din mutanen sun amsa cewa suna da alaka da hukumar leken asirin Pakistan ta ISI.

Kakakin hukumar leken aisirin Afghanistan din Shafiqullah Tahiri ya ce: ''mun same su da kilogram dubu goma na nakiyoyi a Kabul."

A cewar hukumomin dai, da nakiyoyin sun fashe a gari mai jama'a miliyan bakwai da Allah kadai yasan abunda zai faru.

Hukumar leken asirin kasar ta ce tun a makon jiya ne aka cafke mutanen lokacinda aka kai wasu hare hare a Kabul, amma sai yanzu suka bada sanarwa akan lamarin saboda dalilan tsaro.

Mutane hamsin da daya ne suka mutu a harin na Kabul inda dakarun tsaro suka ja daga da 'yan Taliban

Can dama dai Afghanisatan na zargin hukumar leken Asirin Pakistan ta ISI da tallfawa masu tada kayar baya a cikin Afghanistan sai dai Pakistan din tace babu kanshin gaskiya a zargin

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.