Za a tallafawa Asusun Ba da Lamuni na Duniya

Christine Lagarde Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Shugabar Asusun IMF, Christine Lagarde

Kasashe masu bayar da bashi na Kungiyar Kasashe Ashirin Masu Karfin Tattalin Arziki (G20) sun yi alkawarin bayar da rancen kudi sama da dala biliyan dari hudu da talatin ga wani asusun gaggawa na Asusun Bayar da Lamuni na duniya (IMF).

A taron Ministocin Kudi na kungiyar ta G20 a birnin Washington, China tana cikin kasashen da suka yi alkawarin bayar da rancen, kodayake ba ta fadi ko nawa za ta bayar ba.

Wata sanarwa da Babban Bankin China ya bayar ta ce kasar ta China tana da imanin cewa Tarayyar Turai tana da karfin da za ta iya warware matsalar basussukan da suka dabaibaye wadansu kasashen kungiyar.

Ta kara da cewa China tana da imani a kan daidaituwar tattalin arzikin na kasashen Turai.